Sabbin matakan zub da ciki da majalisar dinkin duniya ta mikowa gwamnatin Najeriya
- Takardun da aka kaddamar sun hada da ingantattun hanyoyin zubar da ciki a shari'ance
- MedroxyProgesterone Acetate-Sub Cutaneous (DMPA-SC) Accelerated Scale-up Plan (2018-2022)
- DMPA-SC sabuwar hanya ce ta tsarin iyali da ta hada kwayar maganin hana daukar ciki da kuma allura, wuri daya. Ana sanya shi ne a karkashin fata
UNFPA ta kaddamar da ingantattun hanyoyin zubar da ciki a ranar 4 ga watan yuli, 2018.
Ma'aikatar lafiya ta tarayya tare da hadin guiwar UN population Fund da wasu abokan huldar su a ranar talata sun fitar da ingantattun hanyoyi uku na dokar kiwon lafiya da zai gaggawar kawo tsarin iyali tare da rage mace macen mata masu juna biyu a Najeriya.
Ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewole, wanda Daraktan lafiyar iyali, Dr Adebimpe Adebiyi ya wakilta, ya kaddamar da takardun a Abuja.
DUBA WANNAN: Anyi mare-mare a gidan gwamnati
Takardun da aka kaddamar sun hada da ingantattun hanyoyin zubar da ciki a shari'ance.
MedroxyProgesterone Acetate-Sub Cutaneous (DMPA-SC) Accelerated Scale-up Plan (2018-2022)
DMPA-SC sabuwar hanya ce ta tsarin iyali da ta hada kwayar maganin hana daukar ciki da kuma allura, wuri daya. Ana sanya shi ne a karkashin fata.
Daya takardar da ministan ta kaddamar itace Global Family Planning Visibility and Analytical Network tare da National Logistics Management Information System (NAVISION)
Adewole yace "takardun zasu taimakawa gwamnatin da kuma abokan huldar ta gurin karfafa yunkuri akan tsarin iyali."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng