Siyasar Kaduna: Jerin mutanen da su ka sauya sheka daga Jam’iyyar APC
Mun kawo maku jerin wasu manyan ‘Yan siyasa da su ka sauya sheka daga Jam’iyyar APC mai mulki a Kaduna cikin ‘yan kwanakin nan. Jihar Kaduna na daga cikin inda Jam’iyyar ta fi karfi a Najeriya.
Ga manyan ‘Yan siyasar da yanzu sun koma ko kuma su na daf da shirin komawa Jam’iyyun adawa.
1. Hakeem Baba-Ahmed
Shugaban Jam’iyyar APC na farko bayan kafa ta a Jihar Kaduna Hakeem Baba-Ahmed yana cikin wadanda yanzu su ka tattara su ka bar Jam’iyyar. Baba-Ahmed shi ne Shugaban Ma’aikatan Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya.
2. Ashiru Isa Kudan
Ttsohon ‘Dan Majalisar Jihar Kaduna kuma mai neman Gwamna a Jihar Rt. Hon. Isa Ashiru Muhammad ya bar Jam’iyyar APC mai mulki kwanaki zuwa Jam’iyyar PDP. Isa Ashiru yana cikin manyan Jam’iyyar a Jihar Kaduna.
3. Lawal Adamu Usman
Lawal Adamu Usman wanda aka fi sani da Mr. La ya tattara ya bar Jam’iyyar APC. Matashin wanda yana cikin wadanda aka kafa Jam’iyyar da su yace babu dalilin cigaba da zama a APC saboda irin abin da Gwamnan Jihar yake yi.
4. Haruna Saeed Kajuru
A can kwanaki Haruna Saeed ya bar Jam’iyyar APC mai mulki. Haruna Saeed yayi takarar Gwamnan Kaduna a zaben 2011 a karkashin Jam’iyyar CPC ta Shugaban Buhari inda ya sha kashi hannun Marigayi Patrick Yakowa.
5. Shehu Sani
Fitaccen ‘Dan Majalisar APC mai mulki daga Jihar Kaduna watau Sanata Shehu Sani yace dole su bar Jam’iyyar APC. Ko da Sanatan bai tabbatar da ficewar sa ba amma yace babu wani dalilin cigaban su na zama a Jam’iyyar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng