Za'a kwashi ilimi: Obasanjo ya zama malamin a wata babbar Jami'a a Najeriya

Za'a kwashi ilimi: Obasanjo ya zama malamin a wata babbar Jami'a a Najeriya

- Bayan kammala karatunsa, tsohon shugaban kasar Najeriya ya zama malamin jami'a

- Yanzu haka dai Obasanjo ya shiga cikin sahun shugabannin kasar nan mafi girman takardar karatu

A yau ne tsohon shugaban kasar nan Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar duba ofishinsa a cibiyar karatun jami’ar National Open University of Nigeria dake garin Abeokuta na jihar Ogun bayan ya zama malami a babbar jami’ar karatu daga gida wato (NOUN).

Obasanjo ya zama malamin a wata babbar Jami'a a Najeriya

Shugaban jami’ar NOUN Farfesa Abdalla Uba Adamu

Tun bayan dai kammala karatu digirin digirgir dinsa a jimar’ar ta NOUN, shugaban jami’ar Farfesa Abdalla Uba Adamu ya dauke a matsayin malami a jami’ar.

Obasanjo ya zama malamin a wata babbar Jami'a a Najeriya

Obasanjo ya zama malamin a wata babbar Jami'a a Najeriya

Obasanjo dai shi ne dalibi na farko da ya fara karatun digirin digirgir a jami’ar, inda ya karanci Christian Theology, kuma an bashi takardar shaidar kammala karatu ne a yayin bikin yaye daliban jami’ar karo na bakwai a farkon wannan shekara a Abuja.

KU KARANTA: Martanin hukumar zabe (INEC) kan masu yunkurin yin siyarwa da mutane katin zabe

Darakta mai kula da cibiyar karatun jami’ar dake garin Abeokuta Ibrahim Salawu tare da rakiyar malam makarantar ne suka nunnunawa Dr. Obasanjon sabon ofishin nasa.

Obasanjon ya dai nuna jin dadin tsarin sabon ofishin nasa a jami’ar sannan ya kuma tabbatar da bayar da gudunmawarsa don cigabanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel