Hadimin Buhari ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe akan yan siyasa

Hadimin Buhari ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe akan yan siyasa

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Garba Shehu ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe da ake yi a kasar kan gurbatattun yan siyasa.

Ya ce yan siyasan dake aikata hakan sun kasance wadanda suka daina samun hanyar da za su saci dukiyar kasa.

Mista Shehu, wadda ya ayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayinda yake zantawa da manema labarai ya ce irin wadannan yan siyasansun durkusa domin ganin sun dusashe hasken gwamnatin Buhari.

A cewar Mista Shehu, ana caccakar shugaba Buhari ne musamman saboda yaki da rashawar da yake yi a kasa.

Hadimin Buhari ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe akan yan siyasa
Hadimin Buhari ya daura laifin rashin tsaro da kashe-kashe akan yan siyasa

Don haka hadimin shugaban kasar ya bayyana cea shugaban yayi sa'a saboda ya samu bangaren shari'a dake sabonta kansu sannan kuma suna tare da shi ta fannin yakar cin hanci da rashawa.

Shehu ya kara da cewa shugaban kasar ya toshe duk wata kafa da mutane malalata da yan siyasa ke bi suna sata saboda hakan ne ya sa suke yaki da shi saboda basu ji dadin hakan ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya dawo Abuja bayan taron AU (hotuna)

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin Buhari na gine-gine a fadin kasar.

A cewarsa, babu wata jiha a kasar nan da baza'a samu akalla hanyoyin gwamnatin tarayya guda biyu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng