Nigerian news All categories All tags
An kama wani dan sanda yayi kisa

An kama wani dan sanda yayi kisa

Alkalin kotun majistare ta Ebute Meta dake jihar Legas ta tsare wani sajan din yan sanda, Ishaya Inusa, a gidan yari dake Ikoyi sakamakon zargin shi da ake da kashe wani mutum

An kama wani dan sanda yayi kisa

An kama wani dan sanda yayi kisa

Alkalin kotun majistare ta Ebute Meta dake jihar Legas ta tsare wani sajan din yan sanda, Ishaya Inusa, a gidan yari dake Ikoyi sakamakon zargin shi da ake da kashe wani mutum.

Alkalin kotun, Mrs A.O Adegite, ta kekasa kasa, tayi watsi da rokon da wanda ake zargin da kisan kai.

Ta umarci da a cigaba da tsare shi a gidan kaso kafin ta samu shawara daga daraktan kula da yanke hukunce hukuncen jama'a.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Gambiya ya cire Mataimakiyar sa

Adegite ta dage sauraron karar zuwa 2 ga watan Augusta.

Sifeto Oladele Adebayo, ya sanar da kotun cewa, wanda ake zargin, ya aikata laifin a ranar 11 ga watan Mayu, da tsakar dare.

Abin ya faru ne a Homart Furniture Factory, Ayeteju Elemoro a Ibeju dake Lekki ta Jihar Legas.

Yace wanda ake zargin ya harbi mamacin, Paul Stephen, mai shekaru 24 da bindiga bayan da ya zarge shi da sata.

Adebayo yace laifin ya sabawa sashi na 223 na dokar ta'addanci na jihar Legas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel