Yadda Sojojin Najeriya suka halaka yan Boko Haram 5 a wasu kauyukan Borno
Dakarun runduna ta 112 na Sojojin Najeriya ta yi taho mu gama da wasu mayakan kungiyar Boko Haram a ranar 30 ga watan Yuni a kauyen Andawa na jihar Borno, inda suka halaka guda biyar daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da rauni a jikinsu.
Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun samu nasarar kwace makamai da suka hada da bindigar AK-47, alburusai, da kuma bindigogin toka guda hudu. Haka zalika Sojoji sun yi masayar wuta da yan ta’adda a garin Bama, wanda yayi ajalin mutane biyu fararen hula.
KU KARANTA: Wani Kwarto da kwartuwarsa sun fuskanci tsatstsauran hukunci a Jigawa
A wani labari makamancin wannan, Sojojin Najeriya sun kashe yan Boko Haram guda uku a yayin wani aiki na musamman na kakkabe ragowar yan ta’adda daga jihar Borno, a kauyukan Mallam Kafari, Goni, Alkari, Burbuna da Kantanna, duk a cikin karamar hukumar Munguno.
Daga cikin makaman yan ta’addan da suka kwato akwai bindigar AK-47 guda biyu, Bom daya, da alburusai da dama. Sai dai a yayin wannan artabu, wani Soja guda ya jikkata, wanda a yanzu haka yana samun kulawa a Asibiti.
A wani labari kuma, wani tsohon babban kwamdan Boko Haram, Rawan Goni da a yanzu haka ya tuba ya nemi Sojoji su bashi dama ya kira shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a waya, don ya mika wuya tare da mayakansa guda 137 cikin ruwan sanyi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng