Hukumar 'yan sanda ta cafke wata mata bisa laifin kisan Mijin ta a Jihar Zamfara
Tabbas sai da mai rai ake labarin duniya domin kuwa mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda ta jihar Zamfara ta cafke wata mata, Salamatu Shehu, bisa laifin kashe mijinta a kauyen Rafin-Gona dake karamar hukumar Anka.
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar din da ta gabata kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.
Rahoton da jaridar ta kalato a shafin kamfanin dillancin Labarai na Najeriya ya bayyana cewa, wannan mata dai ta yi amfani da kujerar zama wajen buge Mijinta yayin wata 'yar sa'in sa a tsakanin su, inda nan take ya fadi ba tare da shurawa ba.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan tsautsayi da ganganci gami da karar kwana ya afku ne a ranar 27 ga watan Yunin da ta gabata.
KARANTA KUMA: An tsinto gawawwakin Mutane 23 cikin dokar Daji a jihar Zamfara
A yayin haka kuma hukumar 'yan sandan a ranar Juma'ar da ta gabata ta samu nasarar cafke wani shahararren dan fashi da makami a kauyen Gurusu dake karamar hukumar Bukkuyum a jihar ta Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa, tuni hukumar 'yan sanda ta fantsama cikin bincike domin gurfanar da wannan 'yan ta'adda biyu a gaban kuliya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng