An gurfanar da Matar da ta kekketa Uwardakinta da Reza gaban Kuliya manta sabo
Wata Mata mai shekaru 30, Mariam Amos ta gurfanar a gaban watan Kotun majistri kan tuhumarta da ake yi da kokarin hallaka Uwardakinta da ta bata dakin haya bayan ta kekketata da reza, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai shigar da kara, ASP Ezekiel Ayorinde yana shaida ma Kotu cewar Mariam ta aikata wannan aika aika ne a ranar 12 ga watan Yuni a gidansu dake unguwar Alakuko na jihar Legas.
KU KARANTA: Laftanar Janar Buratai ya kaddamar da madatsar ruwa da Sojoji suka gina a Yobe
Dansandan yace Mariam ta ji ma Uwardakinta mai suna Tolani Sholanke munanan rauni, kawai saboda Tolani ta bata takardar tashi daga gidanta, ma’ana Uwargida Tolani ta kaima yar hayanta Mariam takardar sallama daga gidanta.
Dansandan ya cigaba da cewa Uwargida Tolani ta nemi tasar Marimadaga gidanta ne sakamakon munanan halayyanta, wanda hakan ke yawan kawo rikici tsakaninta da sauran yan hayan gidan.
A cewar Dansandan, laifin da ake tuhumar Mariam ya saba ma sashi na 246 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas, wand aka iya sanadin yanke mata hukuncin zaman gidan Kurkuku na tsawon shekaru uku, idan har aka kamata da laifi.
Sai dai Mariam ta musanta tuhumar da ake yi mata, inda bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkali mai shari;a B.O Osunsanmi ya bada belin wanda ake tuhuma akan kudi naira dubu hamsin, N50,000, tare da mutane biyu da zasu tsaya mata akan dubu hamsin hamsin.
Daga nan sai Alkali Mai shari’a ta dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Yuli.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng