Mata sun fara gwangwajewa da mota a kasar Saudiyya

Mata sun fara gwangwajewa da mota a kasar Saudiyya

A jiya ne dokar da kasar Saudiyya ta saka akan bawa mata damar tuka mota zata fara aiki. An kwashe shekaru masu yawan gaske a kasar ta Saudiyya ba tare da an baiwa mata damar tukin motar ba sai yanzu

Mata sun fara gwangwajewa da mota a kasar Saudiyya

Mata sun fara gwangwajewa da mota a kasar Saudiyya

A jiya ne dokar da kasar Saudiyya ta saka akan bawa mata damar tuka mota zata fara aiki. An kwashe shekaru masu yawan gaske a kasar ta Saudiyya ba tare da an baiwa mata damar tukin motar ba sai yanzu.

DUBA WANNAN: In kana duniya kasha kallo: An gano wani kashin kunkuru mai shekaru miliyan 150 a duniya

Tashar gidan talabijin din Ihbariyya da Al-arabiyya sune suka fitar da wani bidiyo na wata mace ta farko data fara tuka motar a kasar.

A ranar 28 ga watan Satumba ne, sarkin Saudiyya Salman bin Abdul'aziz ya rattaba hannu akan dokar bawa mata damar tuka mota, inda dokar t fara aiki a jiya 24 ga watan Yuni.

Kasar Saudiyya dai tana da burin kawo cigaba ga mata tare da kuma basu aikin yi a shekarar 2030 daga kaso 22 zuwa 30 cikin dari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel