Babbar magana: Kasar Saudiyya ta hana 'yan wannan kasar zuwa Umrah da Hajji

Babbar magana: Kasar Saudiyya ta hana 'yan wannan kasar zuwa Umrah da Hajji

Mahukunta a kasar Qatar dake a yankin gabashin duniya sun zargi kasar Saudiyya da kawayenta da yi masu kullalliyar hana jama'ar kasar su zuwa aikin Hajji da Umara saboda sabanin dake tsakanin su na diflomasiyya.

Wannan zargin dai ya fito ne daga bakin shugaban hukumar dake fafutukar kare hakkin bil'adama a kasar ta Qatar mai suna Ali Bin Smaikh El-Merri lokacin dake yin bayana game da matsayin dangantakar kasashen biyu.

Babbar magana: Kasar Saudiyya ta hana 'yan wannan kasar zuwa Umrah da Hajji
Babbar magana: Kasar Saudiyya ta hana 'yan wannan kasar zuwa Umrah da Hajji

KU KARANTA: Kwallo: 'Yan Najeriya sun fiddo Ahmad Musa takarar shugaban kasa

Legit.ng ta samu cewa yanzu kimanin kusan shekarar daya kenan da kasar ta Saudiyya tare da kawayen ta a yankin na gabas ta tsakiya suka kakabawa kasar Iran takunkumin tattalin arziki.

Sai dai El Merri ya bayyana cewa tuni kasar ta Qatar ta gabatar wani rahoto na musamman a hukumar kare hakkokin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya don ganin an dage takunkumin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel