Masari ya yi alkawarin bayyana Lissafin Kudade na yadda yake tafi da al'amurran Jihar Katsina

Masari ya yi alkawarin bayyana Lissafin Kudade na yadda yake tafi da al'amurran Jihar Katsina

Da sanadin ruwaya ta kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya mun samu rahoton cewa, Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya sha alwashin bayyana cikakken lissafi na kudade dangane da yadda yake gudanar da al'amurran jihar sa.

Masari ya yi wannan furuci ne yayin da Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir ya ziyarci fadar gwamnatin sa yayin bikin Sallah kamar yadda aka saba gudanar da wannan al'ada a ranar Asabar din da ta gabata.

Kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito, gwamna Masari ya bayyana cewa ba zai dakatar da aiwatar da hakan ba zuwa lokuta na neman zabe.

Gwamnan yake cewa, a halin yanzu gwamnatin sa ta kammala kimanin kaso 78 cikin 100 na shiri da tsare-tsaren da ta sha alwashin aiwatar wa ga al'ummar jihar sa.

Masari ya yi alkawarin bayyana Lissafin Kudade na yadda yake tafi da al'amurran Jihar Katsina
Masari ya yi alkawarin bayyana Lissafin Kudade na yadda yake tafi da al'amurran Jihar Katsina

A cewar sa, dukkanin masu tantama kan nasarar gwamnatin sa na iya zuwa gare shi domin duba ga takardu na sheda da zasu tabbatar da hujjojin sa.

KARANTA KUMA: Yadda Ciwon Zuciya ke kassara Maza yayin da suka kai shekaru 40 a Duniya

A nasa jawaban, Sarkin Katsina ya nemi gwamnatin jihar akan ta kara kaimi wajen sanya dokoki da za su magance matsaloli na shaye-shaye fatauci da kuma ta'ammali da muggan kwayoyi a jihar.

Ya kuma jaddada bukatar gwamnatin jihar akan ta dabbaka gaskiya da adalci yayin jagoranci da hakan zai taimaka matuka wajen kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma ci gaba al'ummar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel