Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yiwa matasa huduba mai ratsa jiki
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi wa matasa gargadi a kan shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Sarkin ya yi wannan gargadi ne a jiya Juma'a yayin da ya ke jawabi ga al'umma bayan kammala sallar idi karama da akayi a filin sallar Idi dake kofar mata.
Ya bayyana damuwarsa game da yadda ake kara samun adadin matasa da matan aure da ke shaye-shayen miyagun kwayoyi, ya ce abin ya wuce gona da iri.
KU KARANTA: Sabon salo: Shugabanin jam'iyya sunyi rantsuwa kafafu tsirara
Sarki Sanusi ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya saboda dokar da ta kafa na haramta hadawa da sarrafawa da sayar da magunguna masu dauke da sinadarin codeine a Najeriya.
Ya kuma yi kira ga iyaye su sanya idanu sosai a kan 'ya'yansu da irin wuraren da suke zuwa.
Kazalika, ya yi kira ga al'ummar musulmi su rika yiwa yaransu addu'a na shiriya da sa'a a rayuwa.
Har ila yau, mai martaban ya kuma jadada amfanin zaman lafiya tsakanin mutane inda ya ce sai da zaman lafiya za'a samu bunkasa da cigaba a kasar.
Cikin wadandan suka samu hallartan sallar idin sun hada da gwamna Abdullahi Ganduje da Senata Barau Jibrin da Alafin Oluwa na Iwo, Sarki Abdulrasheed Akanbi da 'yan majalisar tarayya da jiha da kuma manyan jami'an tsaro da sauran manyan mutane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng