Dubun wani dan basaja a matsayin ma’aikacin gwamnati ya cika, har an yi ram da shi

Dubun wani dan basaja a matsayin ma’aikacin gwamnati ya cika, har an yi ram da shi

- Komai nisan jifa masu iya magana suka ce kasa zai fado

- Hakan ce kuwa ta faru ga wani 'dan kasar Togo da ya kware wajen damfarar mutane a matsayin ma'aikacin gwamnati a jihar Legas

- Tuni har ya amsa laifinsa yayin binciken 'yan sanda

Jami'an tsaro sun cafke wani matashi mai shekaru 35 dan asalin kasar Togo wanda yake yin basaja tare da amfani da katin shaidar bogi na ma'aikatan hukumar kula da tsaftar muhalli a Ishodi cikin jihar Legas.

Dubun wani dan basaja a matsayin ma’aikacin gwamnati ya cika, har an yi ram da shi
Kojo.

Jami'an tsaron hadin guiwa na jihar Legas (JTF) sun cafke wannan matashi mai suna Kojo a ranar Juma'ar da ta gabata.

Hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa matashin dan kasar Togo an gan shi ne yana damfarar mutane masu tafiya a kasa a daidai digar jirgin kasa ta Ikeja.

Shugaban hadin guiwar jami'an Sufiritandan ‘yan sanda mai suna Olayinka Egbeyemi ya tabbatar da kama matashi, inda yace an samu nasarar damƙo shi ne bayan da yawaitar ƙorafe-ƙorafe daga mutane daban-daban akan ayyukan da yake yi wanda sun saɓawa doka.

Egbeyemi ya ce an kama matashin ne wanda aka fi sani da 'FRYO' a daidai digar jirgin kasa ta Ikeja, inda aka same shi yana yin damfar, cuta da kuma yin basaja a matsayin jami'in hukumar kula da tsaftar muhalli.

KU KARANTA: Idon wasu ƴan sanda ya raina fata bayan an kama su suna aikata wani abu, karanta kaji

Ya ce mai laifin tare da ire-irensa suna nan suna cin karensu ba babbaka, inda suke kama mutane sannan suce jami'ai ne daga hukumar kula da tsaftar muhalli kuma suna dauke da katin shaidar aiki amma na bogi.

Matashin tare da abokan aikata laifin nasa sukan kama duk wani wanda ya tsallaka titi ba tare da yin amfani da gadar da aka tanada ba domin tsallakawar mutane na ƙafa.

Nan take dai shugaban ‘yan sanda na jihar Legas ya umarci da a gurfanar da shi a gaban kotu domin girbar abinda ya shuka.

Dubun wani dan basaja a matsayin ma’aikacin gwamnati ya cika, har an yi ram da shi
Imohimi Edgal

Mai lefin ya amsa lefinsa na yin amfani da katin Jami'an gwamnati na bogi inda yake karɓar maƙudan kudade daga hannun mutanen da suka karya doka, wanda yace yanzu haka shekarunsa shida yana gudanar da wannan kazamar sana'a ta sa.

Kojo ya bayyana cewa a rana daya yakan samu kudi aƙalla naira dubu 8000 zuwa dubu 10,000 a rana a hannun masu tafiyar ƙafa da suka karya doka kuma ba sa son bata lokaci balle ta kai su ga zuwa kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng