Jami’an Sojojin Najeriya sun kubutar da wasu mutane daga hannun barayin mutane a Kaduna

Jami’an Sojojin Najeriya sun kubutar da wasu mutane daga hannun barayin mutane a Kaduna

- Sojojin Najeriya sun yi artabu da barayin mutane a Kaduna

-Sojoji sun ceto mutane 8 daga hannun masu garkuwa da mutane

Rundunar Sojin Najeriya dake gudanar da aiki na musamman a yankin Brnin Gwari na jihar Kaduna sun yi arangama da wasu miyagu dake satar mutane suna garkuwa da su a kauyen Maidaro na jihar, inda mutum guda daga cikin barayin ya rasa ransa.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar, Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Litinin, 11 ga watan Yuni, inda yace Sojojin sun ceto wasu mutane guda takwas akan hanyar Maganda zuwa Funtua, inda yace a ranar Asabar din da ta gabata ne aka ceto mutanen.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sauka kasar Moroko, an masa tarbar girma

Jami’an Sojojin Najeriya sun kubutar da wasu mutane daga hannun barayin mutane a Kaduna
Mutanen

mutanen da aka ceto sun hada da Maza uku, Mata biyu da kananan yara guda uku, hakazalika Sojojin sun kwato wata mota kirar Golf, Tirela, akwatuna uku dauke da tufafi, bugu da kari yan bindigar sun saki wani babur sun tsere.

Su dai mutanen da aka ceto an sace su ne tun kwanakin baya a daidai hanyar Maganda zuw Sofo dake cikin karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, karamar hukumar da take fama da hare haren yan bindiga, barayin shanu da barayin mutane.

Jami’an Sojojin Najeriya sun kubutar da wasu mutane daga hannun barayin mutane a Kaduna
Motocin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng