Tsige Buhari za mu yi tunda dai shi ba Allah bane – Jagaba
Rahotanni sun kawo cewa wani dan majalisar wakilai, Jagaba Adams Jagaba ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cewar dan majalisar, babu wani abu da ake fuskanta a wannan mulkin baya ga bakar wahala da matsananciyar yunwa.
Jagaba ya kasance dan majalisa mai wakilatar Kachia da Kagarko na jihar Kaduna.
Furucin dan majalisar na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar tayi barazanar tsige shugaba Buhari idan har bai aiwatar da kudurorin da suka zartar ba.
Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa.
Ya jadadda cewa ba sa dari-dari akan yiwuwar hakan saboda "Buharin ba Allah ba ne kuma bai yi kama da Annabi ba, duk inda ya yi kuskure za mu take shi" .
A baya Legit.ng ta rahoto cewa West Idahosa, wani tsohon dan majalisar wakilai, yace sakon da majalisar dokoki ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a warware yake sannan kuma majalisar dattawa na iya ci gaba da shirin tsige shugaban kasar idan yaki basu hadin kai ga bukatarsu.
KU KARANTA KUMA: Saraki da Dogara sun dinke bakunansu akan kujerun marigayi Wakili, Bukar da Jibrin
Idahosa a yayin hira da gidan talbiin din Channels TV shirin Politics Today yace majalisar dokoki na iya ci gaba da shirin tsige shugaba Buhari idan ya ki jin korafin ta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Domin samun ingantattun labaranmu bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng