Idan Buhari bai kakkabe baragurbin dake zagaye da shi ba ba zai tabuka komai ba

Idan Buhari bai kakkabe baragurbin dake zagaye da shi ba ba zai tabuka komai ba

Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mutumin dake da cikakken dattaku da kwarewa wajen iya tafiyar da Najeriya, amm fa mutanen dake zagaye da shi baragurbi ne.

Sani ya bayyana haka ne a yayin hira da gidan talabijin na Channels, inda yace ya san Buhari tun kafin ya zama shugaban kasa, suna tare a jihar Kaduna, kuma ya tabbatar cewar mai gaskiya ne, amma akwai bukatar ya kawar da mutanen dake tare da shi a yanzu.

KU KARANTA: Ba tsoron Allah: Labarin yadda wasu Musulmai ke karyar azuminsu don abin Duniya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan yana kokawa kan yadda Buhari baya daukan mutanen da suka dace a tafiyarsa, haka zalika yace Buhari ya gaza wajen magance kashe kashen da ake yi a arewacin kasar nan.

Idan Buhari bai kakkabe baragurbin dake zagaye da shi ba ba zai tabuka komai ba
Buhari da Shehu Sani

“Gwamnati ta gaza karara wajen hana kashe kashen da ake yi a Arewacin Najeriya, don haka kai ya rabu, kuma yan Najeriya basa ganin kansu a matsayin yan Najeriya, sun fi ganin kansu a matsayin yan kudu, yan Arewa, Musulmai ko Kirista. Ina jiye ma Buhari saboda wannan matsalar kashe kashen za ta bata masa suna a wajen yan Najeriya.” Inji shi.

Sai dai a wani kaolin, Shehu Sani ya yaba da namijin kokarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen yaki da ta’addanci, da kuma yadda take tafiyar da akalar tattalin arzikin kasar, duk da halin da ake ciki.

Daga karshe ya bayyana cewa majalisar dattawa bata da laifi cikin rashin tabbatar da shugaban hukuma EFCC, Ibrahim Magu, inda yace hukumar tsaro ta sirri, DSS, ne ta kai musu rahoton dake nuna Magu ba shi da gaskiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel