Sama da barayi 400 sun tuba a Kano tare da rantsewa da Kur'ani
Rahotanni sun kawo cewa barayi sama da dubu hudu sun tuba a jihar Kano tare da jefar da makaman yakinsu.
Hakan ya faru ne a kananan hukumomin Sumaila da Tudun wada da kuma kwaye inda suka rantse da Al-Kur’ani cewa bazasu sake aikata mumunan aikin ba.
Barayin wadanda sun kai sama da dari hudu, bayan tuban na su, sun ce ba za su sake yin sata ko fashi da makami ba.
KU KARANTA KUMA: 2019: Abunda Arewa zata duba wajen marawa yan takarar shugaban kasa baya - Yakasai
Sun rantse bisa jagorancin Hakimin Sumaila Dan'ruwatan Kano da DPO yan'sanda na Sumaila da 'yan kato da Gora.
Ga sauran hotunan a kasa:
Idan ka na da shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng