Hukumar Sojin Sama ta dauki Sabbin Dakaru 7, 000 cikin shekaru 3
Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, Hukumar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana adadin dakaru da dauka aiki a fadin Najeriya cikin shekaru uku da suka gabata.
Hukumar ta bayyana cewa, ta dauki sabbin dakaru 7, 000 cikin shekaru uku da suka gabata domin inganta harkokin ta na gudanarwa wajen bunkasa tsaro.
Shugaban Hafsin Sojin Sama na kasa, Sadique Abubakar, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai yayin kaddamar da wasu sabbin gine-gine na dakarun ta reshen Shasha dake jihar Legas.
Shugaban dakarun ya kuma sha alwashin ganin karshen kungiyoyin tsageru dake cin Karen su ba bu babbaka musamman a yankunan jihar Legas da kuma kasar Najeriya baki daya.
KARANTA KUMA: 2019: Mashahurancin Shugaba Buhari shi zai tabbatar da Nasarar jam'iyyar APC - Umar Bago
Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar sojin saman cikin 'yan kwanakin ta ci gaba da kaddamar da sabbin gine-gine domin inganta harkokin gudanarwa da kuma jin dadin dakarun ta.
A yayin haka kuma, shuugaban hafsin sojin saman ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da goyon bayan da ya ke ci ga da yi akan dakarun tsaro na kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng