Kannywood za ta dauki nauyin galar fim ta Afirka

Kannywood za ta dauki nauyin galar fim ta Afirka

An fara shirye-shirye karbar bakuncin mahalarta bikin fina-finan da ake shiryawa da harsunan kasashen nahiyar Afirka wanda za'a yi a watan Octoban shekarar 2018 a birnin Kano.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kafa kwamiti gudu uku karkashin inuwar 'Kano Indeginous Languages of Africa Film Market and Festival' (KILAF) wanda aka daura wa alhakin gudanar da shirya bikin.

Za'a gudanar da bikin fina-finan nahiyar Afirka a jihar Kano
Za'a gudanar da bikin fina-finan nahiyar Afirka a jihar Kano

A yayinda ya ke zanatawa da manema labarai bayan kafa kwamitocin, Shugaban Moving Images, Abdulkareem Mohammed wanda shine ciyaman din kwamitin shirye-shiryen ya ce bikin zai bawa yan Afrika daman tallata al'adu da labarun Afirka don yadawa ga sauran kasashen duniya.

KU KARANTA: Dubi yadda zaka iya caje 'dan sanda bayan ya tsare ka a hanya ko yazo maka gida - Hukumar 'Yan sanda

"Muna tsare-tsare don ganin cewa mun inganta fina-finan Afrika yadda mu zamu rika tallata duk wani abu da ya shafi nahiyar Afirka ga sauran kasashen duniya.

"A wannan zamani da duniya ta dunkule waje daya, ya zama dole ko wane al'umma su kasance su ke fadawa sauran duniya labaransu. Idan ka lura da galibin fina-finan da Kannywood keyi, za ka ga muna kwaikwayar al'adun wasu mutane daban ne, domin kawo gyara a harkar ya zama dole mu fahimtar da masu shirya fina-finai rawar da zasu taka wajen tallata al'adun Afrika kamar yadda ta ke," inji shi.

Ya kuma ce bikin zai bawa masu shirya fina-finan daman kara wa juna ilimi da kuma kara musu kwarain gwiwa don rika tallatawa duniya al'adun mutanen nahiyar Afrika.

Malam Sani Mu'azu wani mai shiryawa da bada umurni a masana'antar fina-finan hausa na Najeriya ya ce wannan bikin dama ce ga yan Afirka su tallata fina-finansu ga sauran duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164