Jam’iyyar APC ta caccaki gwamna Rochas, ta gargade shi bayan kiran sa rudadde

Jam’iyyar APC ta caccaki gwamna Rochas, ta gargade shi bayan kiran sa rudadde

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC ya gargadi gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha, day a daina kokarin dora alhakin sabanin dake tsakanin sa da jagororin APC a jihar sa a kan uwar jam’iyya ta kasa.

Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya zargi gwamnan da algungumanci.

Duk da ina ganin girman gwamna Rochas amma dole fadi cewar baya yiwa jam’iyyar APC adalci. Bai kamata ya yi kokarin dorawa uwar jam’iyya alhakin lalacewar dangantaka tsakanin sad a jagororin jam’iyya a jihar sa ba.

Jam’iyyar APC ta caccaki gwamna Rochas, ta gargade shi bayan kiran sa rudadde
Gwamna Rochas

Yin hakan ba daidai bane, tamkar sakawa kauye wuta ne domin a kasha bera. Idan gwamna Okorocha yana da wata damuwa ko matsala a jam’iyyance, kamata ya yi ya zo ya zauna da shugabancin jam’iyya na kasa sabanin ya koma gefe ya yi mana kudin goro,” a cewar Abdullahi.

DUBA WANNAN: Mutane hudu sun mutu a musayar wuta tsakanin 'yan sumogal da jami'an kwastam

Zabukan shugabannin jam'iyyar APC dai sun bar baya da kura. A jihar Edo, shugaba jam'iyyar APC mai barin gado, Cif Odigie-Oyegun bai halarci wurin zabukan ba kamar yadda Kwankwaso da Dogara suka kauracewa wurin zabukan a jihohin su na Kano da Bauchi.

A jihar Delta an kashe wani dan takarar neman zama shugaban jam'iyyar a mazaba ta 1o dake Otu-Jeremi a karamar hukumar Ughelli ta kudu ta hanyar daba masa wuka bayan rikici ya barke yayin gudanar da zabukan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng