Nigerian news All categories All tags
2019: Oladope Agoro ya ba Shugaba Buhari shawara ya koma Daura

2019: Oladope Agoro ya ba Shugaba Buhari shawara ya koma Daura

- Oladope Agoro yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari fa ya gaza

- Dr. Agoro yace Shugaba Buhari ya koma gida kuma shi zai fito takara

- Bayan nan Agoro yace Aisha Buhari za ta zama Mataimakiyar sa a 2019

Mun samu labari cewa Shugaban Kungiyar NAC ta Najeriya Dr. Oladope Agoro ya ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya hakura da neman zarcewa a kan mulki kurum koma gida.

2019: Oladope Agoro ya ba Shugaba Buhari shawara ya koma Daura

Oladope Agoro yace Shugaba Buhari ya koma gona kurum

Oladope Agoro yayi kira ga Shugaban kasar da ya koma gida watau Daura a Jihar Katsina ya huta don kuwa ya gaza yin abin da ake sa rai. Agoro ya fadawa Jaridar New Telegraph a wata hira da yayi cewa ba Shugaba Buhari ke rike da Gwamnati ba.

KU KARANTA: Ana zargin ha'inci a sabon tsarin Shugaba Muhammadu Buhari

Dr. Agoro yake cewa lokacin da zai mulki kasar nan ya zo ko a Jam’iyyar PDP ko kuma cikin Kungiyoyin da tsohon Shugaban kasa Obasanjo yake magana. Agoro yace Shugaba Buhari ba zai yi takara ba don haka zai fito tuta daya da mai dakin sa.

Shi dai Shugaban Kungiyar ta NAC yace da Aisha Buhari zai fito takara kuma Mai gidan na ta Shugaba Buhari ba zai iya kara wani abin kirki ba a kujerar Shugaban kasar. A karshe ya soki dawo da Shugaban Hukumar NHIS da aka yi bakin aiki kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel