Jerin Jihohin da su ke da karancin albarkar kasa a Najeriya

Jerin Jihohin da su ke da karancin albarkar kasa a Najeriya

Kwanakin baya kun ga jerin Jihohin da ke da yalwar kasa a Najeriya. Wannan karo mun kawo maku jerin Jihohin da su ka fi karancin arzikin kasa.

Ga dai jerin Jihohin nan da kuma adadin fadin su na tsawon kilomita:

1. Jihar Legas

A bangaren kasuwanci Legas ce kan gaba a Najeriya amma idan ana maganar filin kasa dai ita ce ta karshe. Legas na da girman da bai wuce kilomita 3, 000 ba saboda yadda ruwa ya mamaye ta.

2. Jihar Anambra

Jihar ta Anambra da ke tsakiyar Kudu maso gabashin kasar ba ta da arzikin kasa. Masana sun ce fadin Jihar Anambra bai wuce kilomita 4, 800 ba. Kusan dai kashi 1% na kasar Zamfara.

3. Jihar Imo

Imo da ke makwabtaka da Jihar Anambra tana da karancin kasa. Jihar Imo da ke Kudancin kasar dai du-du-du ba ta wuce kilomita 5, 500 ba kamar yadda Wikipedia ta bayyana.

4. Jihar Ebonyi

Wata Jiha da ba ta da yalwar kasa ita Ebonyi wanda ita ma ta ke Kudu maso Gabashin kasar. Jihar Ebonyi dai ba ta wuce kilomita 5, 670.

5. Jihar Abia

Ragowar Jihar da ta cika wannan jerin ita ce Abia wanda ita ma ta ke Kudu maso gabashin Kasar. Abia tana da fadin kilomita 6300 ne wanda bai kai fadin karamar Hukumar Kaiama a Kwara ba.

Kwanakin bayan kun ji cewa a girma dai babu kamar Jihar Neja wanda ta kai kimanin kilomiya 76, 000 sannan kuma Jihar Borno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel