Jerin Jihohin da su ka fi arzikin kasa a Najeriya

Jerin Jihohin da su ka fi arzikin kasa a Najeriya

Wannan karo mun shiga cikin batun kasa inda mu ka kawo maku jerin Jihohin da su ka fi arzikin kasa a fadin Najeriya. Duk Najeriya dai babu Jihar da ta kai Jihar Neja fadi wanda za ka iya zuba irin su Legas sama da 20 cikin ta.

Ga dai jerin Jihohin nan da kuma adadin fadin su na tsawon kilomita:

1. Jihar Neja

Jihar Neja ta kai kimanin kilomiya 76, 000 wanda hakan ke nufin ta fi kowace Jiha fadi. Jihar ta yi iyaka da irin su Kasar Kwara da Kaduna da kuma Kasar Sokoto duk ita kadai.

2. Jihar Borno

Borno ta na da tsawon da yah aura kilomita 70, 000 wanda hakan ke nufin ta nunka irin su Jihar Imo da Enugu girman kasa fiye da sau 10.

Jerin Jihohin da su ka fi arzikin kasa a Najeriya
Taswirar Jihohin Najeriya da manyan Birane

KU KARANTA: 2019: Manyan Arewa za su yi wani taro na musamman

3. Jihar Taraba

Shafin Wikpedia ya bayyana cewa Taraba na da fadin Jiha na sama da kilomita 54, 000. Taraba ita ce ta uku a kasar kuma ta nunka Katsina girma sau 2.

4. Jihar Kaduna

Kaduna na da tsawon kasa da yah aura kilomuta 46, 000, jama’a da dama ba su san cewa za a iya zuba Jihar Kano har sau biyu a hada da Legas duk a Kaduna ba.

5. Jihar Bauchi

Allah ya albarkaci Bauchi da filin da ya haura kilomita 45, 000. Bauchi ta fi Legas, da Anambra da Imo da Ebonyi da Abia da Ekiti da Enugu da Akwa-Ibom duk a hade girma.

Sauran Jihohi irin su Yobe, Zamfara, Adamawa, Kwara, Kebbi, Filato da Nasarawa da Katsina ba a bar su a baya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel