Akwai rikici a APC bayan rigima ya barke a wajen zaben Jihar Imo

Akwai rikici a APC bayan rigima ya barke a wajen zaben Jihar Imo

Mun samu labari cewa zaben shugabannin Jam’iyyar APC da aka yi a Ranar Lahadi a fadin kasar nan ya kusa yin sanadiyyar rashin rayuka a Jihar Imo inda wasu manyan Jam’iyyar su ka sha da kyar wanda hakan ta sa Gwamnan ya gana da Shugaba Buhari.

An nemi a tashi jina-jina wajen zaben da aka shirya na shugabannin Jam’iyyar APC a kananan Hukumomin da ke fadin kasar a Jihar Imo. Mataimakin Gwamnan Jihar Price Ee Madumere ma dai da kyar ya ceci kan shi daga ‘Yan daba a wurin.

Na kusa da Gwamnan Jihar mai girma Rochas Okorocha sun koka da cewa an yi abin da abin da bai dace ba wajen zaben makon jiya. Wani daga cikin masu neman Gwamnan kuma surukin Gwamna Okorocha watau Uche Nwosu ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya tattara ya baro Garin Daura

Sanata Benjamin Uwajumogu da kuma wani tsohon Sakataren Gwamnatin Imo Jude Ejiogu da kyar da su ka tsira daga hannun ‘Yan daba a wajen zaben. Akwai dai baraka ne a Jam’iyyar inda wasu da ke bayan Gwamnan su ka kebe su kayi na su zaben.

Dama dai kun ji cewa a Jihar Kano Magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Kwankwaso watau ‘Yan Kwankwasiyya sun yi zaben shugabannin APC dabam da sauran ‘Ya ‘yan Jam’iyyar kuma sun ce za su mika sunayen zuwa uwar Jam'iyya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng