Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin karbe gidajen Patience Jonathan na birnin tarayya

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin karbe gidajen Patience Jonathan na birnin tarayya

- Kotun tarayya dake a birnin tarayya a ranar Litinin ta bayar da umurnin karbe gidaje biyu na matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Gidaje suna a Plot No. 1960, Cadastral Zone A05, Maitama District, da kuma Plot No. 1350, Cadastral Zone A00, duka a birnin tarayya

- Hukumar kula da tattalin arzikin Najeriya (EFCC) a shekarar data gabata sun bukaci a mallaka masu gidajen bisa zargin akwai harkar ta’addanci da keda alaka da gidajen

Kotun tarayya dake a birnin tarayya a ranar Litinin ta bayar da umurnin karbe gidaje biyu na matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Misis Patience Jonathan.

Gidaje suna a Plot No. 1960, Cadastral Zone A05, Maitama District, da kuma Plot No. 1350, Cadastral Zone A00, duka a birnin tarayya.

Gidajen wadanda aka siyesu da sunan Ariwabai Aruera Reachout Foundation, wanda Mrs. Jonathan na daya daga cikin amintattun masu wurin.

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin karbe gidajen Patience Jonathan na birnin tarayya
Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin karbe gidajen Patience Jonathan na birnin tarayya

Hukumar kula da tattalin arzikin Najeriya (EFCC) a shekarar data gabata sun bukaci a mallaka masu gidajen bisa zargin akwai harkar ta’addanci da keda alaka da gidajen, wanda suke bincike akai.

KU KARANTA KUMA: Sanata ya matsa game da shawarar tsige Buhari

Idan bazaku manta ba wannan ba shine karo na farko da kotu ke mallakawa gwamnatin tarayya kadarorin uwargidan tsohon shugaban kasar ba, sakamakon tuhume-tuhume da hukumar EFCC keyiu mata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel