Jerin masu neman takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben 2019

Jerin masu neman takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben 2019

Ana cewa siyasar Kano sai fa Kano, don haka ne wannan karo mu ka kawo maku jerin masu shirin neman takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar adawa watau PDP inda za su kara da Gwamna mai ci.

Jam’iyyar adawa ta PDP har yanzu tana da karfi a Jihar Kano duk da cewa APC ke mulki ta sama da kasa. PDP na da manyan ‘Yan siyasa a Kano irin su tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da mutanen su da su ka bar APC.

Jarin masu neman takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben 2019
Kwankwaso ya samu sabani da Ganduje a Jihar Kano

Yanzu haka dai ‘Yan Kwankwasiyya sun bangare daga Jam’iyyar APC bayan an samu sabani tsakanin Gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon Mai-gidan sa kuma Sanata a yanzu Rabiu Musa Kwankwaso.

KU KARANTA: 'Ya 'yan tsofaffin 'Yan siyasan Kano na neman kujera

Daga cikin masu neman Gwamnan a zaben 2019 akwai wasu tsofaffin Kwamishinonin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau da kuma ‘Dan takarar Gwamnan a Jam’iyyar ANPP a 2011 da kuma wasu ‘Ya ‘yan manya a Jihar ta Kano.

Masu harin kujerar dai sun haura 10 ga kuma sunayen su nan:

1. Alhaji Salihu Sagir Takai

2. Dr Umar Musa Mustapha (Mai Mustaleta)

3. Bello Sani Gwarzo

4. Alhaji Mamuda Sani Madakin Gini

5. Alhaji Garba Yusuf

6. Alhaji Jafar Sani Bello

7. Alhaji Sadiq Aminu Wali

8. Alhaji Abdullahi Sarki Yakasai

9. Alhaji Nasiru Madina Fagge

10. Alhaji Ahmed S. Aruwa

11. Injiniya Sarki Labaran

12. Alhaji Nasiru Muhammad.

Kwanakin baya masu harin kujerar Dr. Abdullahi Ganduje su ka yi wani taro inda Shugaban Jam’iyyar adawar na Jihar Kano Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa ya jagoranta inda ya nemi ‘Ya ‘yan Jam’iyyar su hada kai ayi aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel