Gwamna Ganduje ya amince a karawa Ma’aikatan Kano albashi

Gwamna Ganduje ya amince a karawa Ma’aikatan Kano albashi

- Gwamnan Kano na shirin karawa Ma’aikatan Jihar sa albashi

- Abdullahi Ganduje ya kara Miliyan 88 cikin abin da yake biya

- Ma’aikatan Jihar na lashe sama da Naira Biliyan 9.2 a duk wata

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya amince a karawa Ma’aikatan Jihar sa albashi inda yanzu ya amince da a cire wasu makudan kudi domin biyan Ma’aikatan.

Gwamna Ganduje ya amince a karawa Ma’aikatan Kano albashi
Gwamnan Kano zai karawa Ma’aikata albashi bana

Labari ya zo mana daga Jaridun Kasar nan ta bakin Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano watau Alhaji Auwal Na-Iya cewa Gwamnan Jihar ya amince a fitar da kudi har Naira Miliyan 88.9 domin a karawa ma’aikata albashi.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya na zargin Zakzaky da kisan-kai

A halin yanzu dai Jihar Kano na biyan Ma’aikatan ta albashin da duk wata ya ke lashe sama da Naira Biliyan 9.2. Alhaji Na-Iya ya bayyanawa wasu da su ka kai masa ziyara ewwa daga watan nan za a samu karin albashi a Jihar.

Shugaban Hukumar NIM na tattali Dr. Abubakar Sallisu yayi jawabi a lokacin ziyarar inda ya nemi damar su karbi masaukin baki a wani gagarumin taro da aka shirya na kasa baki daya a cikin Jihar Kano a kwanan nan.

A Jihar Kano dai mun rahoto maku cewa kwanan nan ne Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano ta yaye ‘Dalibai sama da 8000 na kakar karatun shekarar 2017 da 2018. Daga ciki an samu wasu zakukuran gaske kadan da su ka ciri tuta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng