Wani limami 'dan Najeriya ya tsinci kudi mai yawa a Saudiyya, ya mayar dasu saboda tsoron Allah
- Wani mutum ya nuna halin dattako a lokacin da yaje aikin hajji a Makka
- Mutumin wanda ya kasance limami a Najeriya ya dawo mayar da wata jaka makare da kudi ga 'yan sanda a Saudiyya
- Limamin ya nuna hoton jakar kudin daya tsinta a shafin sada zumunta na Facebook
Legit.ng taci karo da wani labari da ke nuna irin halin gaskiya da dattaku na yan Najeriya. Wani mutum dan Najeriya ya nuna tsantsar amana da dattako ta hanyar mayar wa hukuma jakar kudin da ya tsinta a kasar Saudiyya a lokacin da yaje aikin hajji.
Mutumin wanda ya kasance limami ne ya bayyana wa duniya yanda ya tsinci jakar makare da kudi. Limamin wanda akafi sani da Ejolunibo Ganiyu ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook.
Ganiyu yace ya tsinci jakar ne bayan kammala sallolinsa a can kasa me tsarki. Mutumin ya kasance mai gaskiya wanda a take ya kira hukumar yan sanda domin a nemo mai jakar mika masa abarsa.
DUBA WANNAN: Wata sabuwar rikici ta barke a Nasarawa, mutane 15 sun riga mu gidan gaskiya
Ganiyu yace jami'in dan sandan ya nuna tsantsar mamakin sa akan mayar da kudin da yayi saboda baiyi tsamanin dan Najeriya zai tsinta kudi kuma ya mayar dashi ba.
Kalamansa "A yau bayan sallar azahar na batar da wayata wani mutum ya tsinta ya kawomin, na shirya na fita domin gabatar da sallar magariba tare da wasu mutane hudu da muke tafiya tare, a lokacin ne na tsinci wannan jaka sai nayi tunanin Allah shine abin tsoro sama da wannan kudi, sai nakira jami'in dan sandan na bashi wanda yayi matukar mamakin dan nageriya ya dawo da irin wadannan kudi masu yawa sannan yayimin godiya, ga hoton kudin nan. Allah ya saka mana da alkhairi ya hadamu a aljannar firdausi ma'assalam"
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng