Dakarun soji sun cafke wasu gagararrun masu garkuwa da mutane a Kaduna, duba hotunan su
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane a Kaduna yayin wani sintiria a Rijana.
Wadanda aka kama din har yanzu na tsare a hannun hukumar soji inda ake kara tsananta bincike a kansu.
A wani labarin mai alaka da wannan, rundunar hukumar soji ta 72 tayi nasarar dawo da zaman lafiya a Otukpo dake jihar Benuwe bayan barkewar wata jimurda bayan wasu 'yan bindiga sun kutsa kai cikin wani wurin taron siyasa inda suka bude wuta.
A yayin da 'ya'yan jam'iyyar APC ke tsaka da gudanar da taro ne a wani Otal dake kan titin Otukpo, wasu 'yan bindiga suka kutsa kai suka bude masu wuta tare da kashe mutane biyu tare da jikkata wani mutum guda.
DUBA WANNAN: Anyi wani karon batta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram, an rasa rayuka a kowanne bangare
Jami'an soji sun mamaye yankin da abin ya faru domin hana barkewar karin wani rikicin.
Rundunar soji ta 101 na cigaba da sintiri a karamar hukumar Suntai da kewaye domin cigaba da kakkabe batagari dake tayar da hankula a jihar.
Darektan hulda da jama'a na hukumar soji, Texas Chukwu, ya fitar da wannan sanarwa tare da bukatar jama'a su sanar da hukumar duk wani motsi da basu yarda da shi ba ko yunkurin tayar da hankalin al'umma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng