Kwankwaso ya tafi ya bar mana bashin Naira Biliyan 300 – Inji Jihar Kano

Kwankwaso ya tafi ya bar mana bashin Naira Biliyan 300 – Inji Jihar Kano

- Ganduje yace Kwankwaso ya bar masa bashi har Biliyan 300 a Kano

- Gwamnan yace duk da haka wannan dai bai hana shi aiki a Jihar ba

- Gwamna Ganduje yace su na aiki kuma su na biyan bashin da aka ci

Jiya ne mu ka ji cewa Jaridar Daily Trust yi hira da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana yawan bashin da tsohon Gwamnan Jihar watau Rabiu Kwankwaso ya bari. Ganduje yace hakan bai hana shi yi wa jama’a aiki ba.

Kwankwaso ya tafi ya bar mana bashin Naira Biliyan 300 – Inji Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano Ganduje yace yana biyan bashi kuma yana aiki

Mai Girma Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje yace ya gaji bashin Naira Biliyan 300 daga Gwamnatin baya. Sai dai Ganduje wanda shi ne Mataimakin Kwankwaso a wancan Gwamnati yace hakan bai kawowa Gwamnatin na Kano matsala ba.

Ganduje yace a wancan lokacin da ake shirin damka masa mulki, ya fito ya bayyana cewa bashin da Gwamnatin su ta Kwankwaso ta ci ba matsala bane saboda gudun a samu matsala. Ganduje yayi alkawarin zai cigab daga inda aka tsaya.

KU KARANTA: Abin da ya sa 'Yan Majalisa ke da bakin jini a Najeriya

Duk da wannan ‘dan-karen bashi dai Gwamna Ganduje bai fasa ayyukan sa ba. Gwamnatin Ganduje ta cigaba kamar yadda Kwankwaso yayi kokari wajen gyara Jihar. Ganduje dai ya karasa har wasu ayyukan tsohon Gwamna Shekarau.

Kwanaki dama kun ji cewa tsohon Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso yayi nasara a Kotu ina ake kalubalantar tikitin da ya samu na Sanata a karkashin Jam'iyyar APC a 2014.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng