Wani matashi ya yi ma Budurwarsa wanka da ruwan guba kan zarginta da neman maza
Wata budurwa mai shekaru 27, Toyin Busari na fuskantar matsananciyar wahala a sakamakon watsa mata ruwan guba da saurayinta Lukman Madoti yayi a jihar Legas, inji rahoton jaridar Punch.
A yanzu haka, Toyin, wanda yar kasuwa ce a kasuwar Akala dake unguwar Mushin na jihar Legas na kwance cikin halin rai fakwai mutu fakwai a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas, dake Gbagada.
KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a Benuwe, sun kashe Dagaci
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lukman, wanda shi ne shugaban yan Achabar unguwar ya zargi Toyin ne da laifin bin maza, da wannan ne zafin kishi ya kwashe shin, inda har ta dauki wannan mummunan mataki akanta, sai dai tuni Yansanda sun cika hannu da shi.
Sai dai na kusa dasu su tabbatar da cewar an sha samun rikici a tsakanin masoyan, tun bayan haduwarsu kimanin shekara guda da ya gabata, duk saboda rashin aminta da juna, wannan sabon rikicin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 10 bayan dawowar Toyon daga garinsu, a can jihar Oyo, inda taje don duba mahaifiyarta.
Sai da makwabta suka shiga tsakaninsu a wannan dare, sakamakon dambacewa da suka yi da juna, wand ta kai ga Lukman kwace wayar hannun Toyin, amma ashe Lukman bai hakura ba, inda ya sadada dakin Toyin da asubah, ya watsa mata ruwan guba, ia ranta ana kare.
Allah ya sa akwai jama’an da suka jiyo ihun Toyin, inda suka bi sawun Lukman, suka samu nasarar cafke shi, suka lakada masa dan banzan duka, sa’annan daga bisani suka mika shi ga jami’an Yansanda.
Kaakakin rundunar Yansandan jihar SP Chike Oti ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace a yanzu haka Toyin ta fara farfadowa sakamakon kulawa ingantacce da ta samu daga Likitocin Asibtin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng