Kalli bidiyon lugaden wuta da Sojin Saman Najeriya da Nijar sukayi wa 'yan Boko Haram

Kalli bidiyon lugaden wuta da Sojin Saman Najeriya da Nijar sukayi wa 'yan Boko Haram

- Sojin saman Najeriya sunyi hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Nijar inda suka kaiwa yan Boko Haram wata mummunan hari

- Sijin Najeriya sunce an kai harin ne sakamakon bayannan sirri da aka samu daga Sojin saman kasar Nijar

- An kuma yi nasarar kashe wasu daga cikin yan ta'addan da sukayi kokarin tserewa bayan an kai harin

Hukumar Sojin Saman Najeriya karkashin Operation Dole tare da Sojin saman kasar Nijar sunyi nasarar kai wata harin bama-bamai akan yan ta'addan Boko Haram da ke buya a yankin Aregu da Tumbun Rago da ke jihar Borno.

An kai harin ne a ranar 8 ga watan Aprilu, inda hukumar sojin na Najeriya tace anyi nasara. An kai harin ne bayan bayannan sirri da daukan hotunnan bincike don tabbatar da kasancewar 'yan ta'addan wanda akayi ta hanyar amfani da wani jirgin leken asiri na sojin saman Najeriya.

Kalli bidiyon lugaden wuta da Sojin Saman Najeriya da na Nijar sukayi wa 'yan Boko Haram
Kalli bidiyon lugaden wuta da Sojin Saman Najeriya da na Nijar sukayi wa 'yan Boko Haram

Kamar yadda sanarwan data fito daga direktan hulda da jama'a na Sojin saman, Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ta bayyana, an kai harin ne a yankunan Arege da Tumbun Rago da ke jihar Borno.

Kalli bidiyon a kasa.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa Sojin saman Najeriya sun tsananta kai hare-hare ta sama a yankin arewa maso gabashin Najeriya inda suka kashe dimbin yan ta'adda a Tumbin Rago, wata kauye da ke kan iyakar Najeriya da tafkin Chadi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164