Jerin Gwamnonin da za su bar kujerar su zuwa shekarar 2019
A Najeriya akwai Gwamnonin da zuwa ko kafin 2019 za su tattara su bar kujeran su dalilin kammala wa’adin su da su kayi na shekaru 8 a kan gadon mulki. Wannan karo mun kawo maku jerin wadannan Gwamnoni masu shirin barin gado.

Gwamnan Borno Kashim Shettima wanda shi ne Shugaban Gwamnonin Arewa zai bar kujera a 2019 bayan yayi shekaru 8 yana kan kujerar Gwamna.
2. Ayo Fayose
Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti zai bar kujera a bana bayan a da can yayi mulki na shekaru 4 a lokacin tsohon Shugaban kasa Obasanjo kafin a tsige sa.
KU KARANTA: EFCC ta gano yadda jami’an Gwamnati ke satar dukiyar al’umma
3. Ibrahim Dankwambo
Gwamnan Gombe shi kadai ne wanda ya lashe zabe a karkashin PDP a Arewacin Najeriya kuma babu mamaki yayi harin takarar kujerar Shugaban kasa a 2019.
4. Abdulfatah Ahmed
Gwamna Abdulfatahi na Jihar Kwara zai kammala wa’adin sa ne a 2019. Tsohon Kwamishinan ya zama Gwamna ne bayan Bukola Saraki yayi shekaru 8.
5. Ibekunle Amosun
Gwamnan Jihar Ogun Amosun zai kammala wa’adin sa a 2019 bayan ya samu tazarce a zaben 2015 a karkashin Jam’iyyar APC.
Gwamnan na Jihar Osun zai kammala wa’adin sa ne kafin zaben 2019 don kuwa ya hau Gwamna ne a 2010 kuma ya samu zarcewa a 2014.
7. Abiola Ajimobi
Abiola Ajimobi dai kamar ‘danuwan sa Gwamnan Jihar Ogun Amosun zai bar kujerar sa ne na Gwamnan Jihar Oyo a zaben 2019 tun da yayi shekaru 8.
8. Ibrahim Geidam
An rantsar da Gwamna Geidam na Jihar Yobe kusan sau 3 a tarihi bayan ya gaji marigayi tsohon Gwamna Mamman Ali zai kuma cika wa’adin sa a 2019.
9. Tanko Al-Makura
Gwamnan Nasarawa Al-Makura ya hau kujera ne a karkashin CPC a 2011 kafin ta koma APC. Shi ma wa’adin sa zai kare a shekarar 2019.
10. Rochas Okorocha
Gwamnan Imo kuma Shugaban Gwamnonin APC watau Okorocha zai bar gadon mulki a 2019 inda ya ke saran kakaba surukin sa a kujerar.
11. Abdulaziz Yari
Shugaban Gwamnonin Najeriya Yari zai cika shekarun sa 8 a kan mulki ne a 2019 bayan ya karbi kujerar daga hannun Mahmud Shinkafa a 2011.
Irin su Henry Dickson za su kai har 2020 a mulki da kuma Willie Obiano da su ka lashe zabe a bara za su cigaba da zama kan mulki har nan da shekaru 4 masu zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng