Yanzu-Yanzu: 'Yan kunan bakin wake 3 sun mutu a Maiduguri - NEMA

Yanzu-Yanzu: 'Yan kunan bakin wake 3 sun mutu a Maiduguri - NEMA

- 'Yan kunan bakin wake guda uku sun mutu a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno

- Hukumar bayar da agajin gagawa NEMA ce ta bayar da wannan sanarwan

- An tayar da mayan bama-bamai guda hudu a garin na Maiduguri a jiya Juma'a 30 ga watan Maris

Hukumar bayar da agajin gagawa na kasa (NEMA) ta tabbatar da cewa wasu yan kunan bakin wake guda uku da sukayi kokarin shiga kauyen Muna da kai garin Maiduguri sun gamu da ajalinsu a ranar Juma'a 30 ga watan Maris.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa wasu manyan bama-bamai guda hudu sun fashe tsakanin karfe 9 zuwa 9.30 na daren Juma'a wanda hakan ya jefa garin cikin dimuya da fargaba.

Yanzu-Yanzu: An kashe 'yan kunan bakin wake 3 a Maiduguri - NEMA
Yanzu-Yanzu: An kashe 'yan kunan bakin wake 3 a Maiduguri - NEMA

Mai kula da harkokin hukumar ta NEMA na yankin arewa maso gabas, Mr. Bashir Garga ne ya tabbatar da tashin bama-bamai a cikin garin na Maiduguri.

Garga ya bayyana cewa yan kunan bakin waken da ke dauke da bama-baman a jikinsu sun mutu ne yayin da bam din ya fashe a jikin su kafin su tsallako ganuwar da aka gina saboda tsaro a garin na Muna.

KU KARANTA: An rasa rayuka 5, wasu 13 sun jikkata a wani sabon harin bam da aka kai Maiduguri

Ya ce karar fashewar bama-baman ne ya sanya wasu mutane suka rikice kuma suka sami raunuka wajen guje-guje. Garga ya kara da cewa dukkan wanda suka sami raunuka suna karban magani a asibiti a halin yanzu.

"Har yanzu akwai sauran bayyanan da bamu gama samu ba don fashewar bam din ta faru ne a wajen ganuwar garin na Muna kuma yan kunan bakin waken ne kawai suka mutu," inji shi.

NAN ta ruwaito cewa tashar garin Muna yana daya daga cikin wuraren da 'yan ta'adda suka fi kawo harin bama-bamai hakan ma ya sa aka sanya dokar hana yawo a wannan yankin don tabbatar da tsaro.

A ranar Asabar 15 ga watan Maris, Hukumar Yan sanda ta gargadi al'ummar jihar Borno da cewa akwai yiwuwar yan ta'addan zasu kawo harin bam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel