'Yan sanda sun kwace makamai 198 daga daga hannun makiyaya da barayin shanu a jihar Katsina
Hukumar 'yan sanda Najeriya a jihar Katsina ta ce tayi nasarar kwato makamai a kalla 198 daga hannun makiyaya da barayin shanu a jihar.
Mohammed Wakili, kwamishinan 'yan sanda a jihar, ya sanar da hakan yayin taro da manema labarai a jihar, yau, Laraba.
Ya ce hukumar ta mayar da hankali wajen kwato makaman ne biyo bayan umarnin da Sifeton 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya bayar ga kwamishinonin 'yan sanda na jihohi da mataimakansa dake shiyyoyin kasar nan.
Ya kara da cewar mafi yawan makaman an kwato su ne daga hannun makiyaya da barayin shanu da ragowar 'yan ta'adda.
Wakili ya ce, makaman sun hada da bindiga kirar AK-47 guda 20, karamar bindiga guda 10, manyan bindigu guda 8 da wasu bindigu kirar SMG guda biyu.
DUBA WANNAN: Da Duminsa: 'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, sun kashe mutane dama
Ragowar sun hada da bindigun fistol kirar gida guda 70, bindigar baushe 80, da alburusai masu yawa.
Ya bayar da tabbacin cewar jami'an 'yan sanda zasu cigaba da farautar makamai dake hannun farar hula tare da yin kira ga wadanda suka mallakai makamai da su dawo da su kafin cikar wa'adin da hukumar ta diba masu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng