Mutane shida sun shiga hannu bayan dukan dan sanda bisa zargin satar al'aura

Mutane shida sun shiga hannu bayan dukan dan sanda bisa zargin satar al'aura

- An gurfanar da mutane shida gaban kotun majistare dake Igbosere a jihar Legas

- Ana tuhumar su da lakadawa wani dan sanda dukan kawo wuka tare da yin lahani ga wani dan asalin Kotono

- Wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin da ake zarginsu da shi

An gurfanar da wasu mutane shida gaban kotun majistare dake Igbosere a jihar Legas biyo bayan yin lahani ga wani kuku dan kasar Kotono tare da yiwa wani jami'in dan sanda dukan kawo wuka.

Wadanda ake tuhumar; Babagana Mustapha; direban adaidaita sahu, da abokansa guda biyar; Isa Hassan, Kari Kambo, Bulu Umar, Alhaji Mustapha, da Isma'il Babagana, sun zargi kuku, Mickey Dauwo; dan asalin kasar Kotono, da sacewa Mustapha al'aura.

Mutane shida sun shiga hannu bayan dukan dan sanda bisa zargin satar al'aura
Mutane shida sun shiga hannu bayan dukan dan sanda bisa zargin satar al'aura

Dan sanda mai gabatar da kara, Saja Reuben Solomon, ya ce, a ranar 14 ga watan Maris, da misalin karfe 12:30 na rana, a kan titin Saka Tinubu dake unguwar Victoria Island a jihar Legas, Mustapha ya zargi Dauwo da sace masa al'aura bayan ya nemi canjin N100 a wurinsa.

Dan sandan ya kara da cewa, Mustapha ya yi haka ne domin yaudarar Dauwo ya bi shi domin zuwa wurin likitan da zai tabbatar al'aurar Mustapha bata bata ba. Amma maimakon su wuce asibitin sai ya tafi da shi ya zuwa wani kango inda ragowar mutane biyar din ke jiransa, kuma da zuwansu su ka far wa Dauwo da sara da suka.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane, sun kwato likitocin da aka sace

A yayin da suke dukansa ne sai jami'in dan sanda, Balogun Gideon, ya kawo agaji bayan jin ihun Dauwo yayin da yake wucewa ta kusa da kangon. Saidai mutanen sun lakadawa shi ma jami'in dan sandan duka tare da ji masa raunuka.

Ana tuhumar su da aikata laifuka uku da su ka hada da; hadin baki, cin zarafi, da tayar da hankali.

Ma su laifin sun musanta tuhumar da ake yi ma su.

Alkalin kotun, Mai shari'a Davis, ya bayar da su beli a kan kudi N120,000 kowanne mutum sanna ya daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng