MURIC tayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaban kasa Buhari game da batun barace-barace a Arewa

MURIC tayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaban kasa Buhari game da batun barace-barace a Arewa

- Wata Kungiya tace ya kamata Gwamnatin nan ta kawo karshen Almajiranci

- MURIC ta nemi Shugaba Buhari yayi koyi da tsohon Shugaban kasa Jonathan

- Kungiyar tace Gwamnonin Arewa ba su da niyyar kawo karshen matsalar nan

Wata Kungiyar Musulmai mai suna MURIC tayi kaca-kaca da Gwamnonin Arewa na Gwamnatin Shugaban kasa Buhari inda tace ba su da niyyar kawo karshen Almajiranci a Yankin wanda sai an kauda su za a ga karshen Boko Haram.

MURIC tayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaban kasa Buhari game da batun barace-barace a Arewa
Ya kamata Gwamnatin nan ta kawo karshen Almajiranci inji Kungiyar Musulmai

Shugaban Kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar inda yake mai yabawa Gwamnatin tsohon Shugaba Jonathan na kokarin kawo karshen Almajiranci ta hanyar gina makarantun Al-majirai a Yankin.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi magana game da batun IGP na 'Yan Sanda

Yanzu dai wadannan makarantu da Jonathan ya bude sun kama hanyar lalacewa don haka aka nemi Gwamnatin Shugaba Buhari tayi wani abu kan batun almajirai wanda su ka haura Miliyan 10 kuma ana amfani da wasu wajen aikin assha a kasar.

An dai samo asalin Almajirai ne tun daga lokacin da Manzon tsira Annabi Muhammad SAW yayi hijira. Sai dai a Najeriya an maida abin hanyar bara inda iyaye ke jefar da yaran su da sunan karatu a kan titi cikin yunwa da ruwan sama da kazanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng