An kashe mutane 3 a sabon hari da aka kai kauyen Katsina

An kashe mutane 3 a sabon hari da aka kai kauyen Katsina

Rahotanni sun kawo cewa an kashe yan fashi biyu da wani dan gari bayan wasu barayi sun kai hari kauyen Tandama dake karamar hukumar Danja dake jihar Katsina.

A cewar wani idon shaida wanda yan fashin suka kashe dan uwansa misalin karfe 1:15 na tsakar dare, wasu mutane sanye da kayan sojoji da bindigogin AK 47 sun kai farmaki gidan wani Abdullahi Tandama da Alhaji Sufyanu.

Sai dai hadin gwiwar mazauna garin yayi sanadiyar mutuwar biyu daga cikin yan bangan bayan sun kashe wani mazaunin yankin.

An kashe mutane 3 a sabon hari da aka kai kauyen Katsina

An kashe mutane 3 a sabon hari da aka kai kauyen Katsina

“Dan uwana da wasu tsiraru na kwance a wajen gidanmu amma karan harbin bindiga ya tashe su inda suka yi kokarin taimako amma sai daga baya aka kashe shi, duk da cewan bamu da bindigogi, mun far masu da kibiya, mun kashe biyu daga cikinsu kafin su gudu bayan sun ji zuwan yan sanda”.

KU KARANTA KUMA: Harin Adamawa: Sojoji sunyi arangama da makiyaya, mutane 10 sun mutu

A halin da ake ciki, rundunar yan sandan Katsina a wata sanarwa ga manema labarai tace yan fashin sunyi arangama da yan sanda wanda yayi sanadiyan mutuwar biyu daga cikinsu.

A halin da ake ciki dakarun sojoji sun arangama tare da kashe wasu mutane 10 da ake zargin makiyaya ne bayan sun kai hari kauyen Gwamba dake karamar hukumar Demsa na jihar Adamawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel