An gurfanar da barayin da suka ketara katangar ma'aikatar kasafin kudin jiha domin satar kudi
- Wasu mutane biyu da suka shiga ofishin kasafi domin satar kudi a jihar Legas sun shiga hannu
- Dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotu cewar mutane biyun da ake zargi sun shiga ginin ma'aikatar ne ta silin
- Wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake masu
An gurfanar da wasu mutane biyu gaban wata kotun majistare dake Ikeja ta jihar Legas bisa da shiga ma'aikatar kasafin kudi ta jihar domin yin sata.
Wadanda ake zargin; Sunday Igili; mai shekaru 50 da Simon Akan; maj shekaru 40 na fuskantar caji guda biyu da suka hada da hadin baki domin aikata laifi da kuma shiga inda basu da hurumi.
Dan sanda mai gabatar da kara, Matthew Akhaluode, ya shaidawa kotu cewar wadanda ake zargin sun shiga ginin ta silin din bandakin ma'aikatar da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu.
KARANTA WANNAN: Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar kundin shari'ar Najeriya ya tanadi hukuncin daurin shekara uku ga ketara gidan da ba na mutum ba da kuma daurin shekara biyu ga hadin baki domin aikata laifi.
Wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake masu.
Alkalin kotun, Y. R. Pinheniro, ya bayar da su beli a kan N100,000 da masu tsaya masu mutum biyu kowanne su. Kazalika ya daga sauraron karar ya 12 ga watan Maris.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng