Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ofishin sashen jam’iyyar APC da ta dakatar da El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ofishin sashen jam’iyyar APC da ta dakatar da El-Rufai

- Gwamnatin Kaduna ta rusa ofishin sashen jam’iyyar APC da ta dakatar da El-Rufai na tsawon watanni shida

- Magoya bayan Sanata Suleiman Hunkuyi suna zargin gwamna Kaduna da daukan nauyin rusa musu ofishi

Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa Hedkwatar sashin jam’iyyar APC da ta dakatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, har na tsawon watanni shida.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, an rusa ofishin ne dake gida mai lamba 11B, Sambo road, GRA Kaduna,da kariyan jami’an tsaro da misalin karfe 4 na safiyan ranar Talata.

Sashen APC dake Adawa da El-Rufai suna kiran kansu da sunan, Kaduna Restoration group, wanda karkashin jagorancin sanata Suleiman Hunkuyi.

Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ofishin sashen jam’iyyar APC da ta dakatar da El-Rufai
Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ofishin sashen jam’iyyar APC da ta dakatar da El-Rufai

Wasu magoya bayan, Sanata mai wakiltar mazabar Arewacin Kaduna, Suleiman Hunkuyi sun zargi gwamna, Nasir El-Rufai, da daukar nauyin rusa musu ofishin su.

KU KARANTA : Hukumar NHIS za ta maida hankali ne wajen yi wa jama’a aiki – Yusuf Usman

Har yanzu gwamnan jihar Kaduna bai ce komai ba game da wannan al’amari ba.

Wani babban jami'in hukumar kula da tsarin garin kaduna (KASUPDA) wanda bai son a bayyana sunan sa, ya fadawa manema labaru cewa ba ruwan gwamnatin jihar Kaduna akan wannan al’amari, aikin su kadai suke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng