Yadda na karbi Musulunci bayan na ji karatun Al-Kurani
- Wata Baiwar Allah ta karbi addinin Musulunci a kasar Columbia
- Kasar ta Columbia na cikin inda ake fama da karancin Musulmai
- Karatun Al-Kura’ni ya sa ta bar Kiristanci ta karbi addinin Islama
Wata tsohuwar Kirista tayi ridda ta bar addinin na ta kuma ta bayyana abin da ya sa ta shiga addinin na Musulunci. Wannan abu ya faru ne a Kasar Columbia inda ake fama da karancin Musulmai.
Jessica Johanna wata Baiwar Allah da ke karatu a wata Jamia'a a Kasar Columbia tayi amfani da shafin tambayoyi da amsoshi na kafar zamani watau Quora inda ta kawo dalilin da ya sa ta dawo Musulma bayan da tana Kirista.
KU KARANTA: Abin da ke hana 'Daliban Najeriya cin jarrabawa
Johanna tace wata kawarta ce ta fara kai ta wani Masallaci inda ake karatun Larabci da Al-Kurani kuma tun daga nan ta fara gane gaskiya. Johanna tace dama can ta san Yesu ba Ubangiji bane sai dai ace Manzon Allah mai girma.
Wata rana Baiwar Allah tana Kasar Morocca sai ta ji karatun Al-Kurani a lokacin azumi tun daga nan imani ya shige ta. Tana dawowa gida kuwa tace sai ta karbi addinin Musulunci bayan tayi kalmar shahada.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng