Shugaba Buhari ya rokawa ‘Yan kasuwar Kano Allah ya maida alheri

Shugaba Buhari ya rokawa ‘Yan kasuwar Kano Allah ya maida alheri

- A ranar Asabar ne gobara ta auka kasuwar ‘Yankifi a Kano

- Shugaba Buhari ya aikawa mutanen kasuwar jaje dazu nan

- Shugaban kasar yayi addu’a Allah ya maida alheri nan gaba

Labari ya zo mana cewa Shugaban Kasa Muhammmadu Buhari ya rokawa ‘Yan kasuwar Kano Allah game da masifar da ta auka masu na gobara a wata kasuwa da ke cikin Garin kwanan nan.

Shugaba Buhari ya rokawa ‘Yan kasuwar Kano Allah ya maida alheri
Na san zafin mutum ya rasa gumin sa inji Shugaba Buhari

Shugaba Muhamamadu Buhari da bakin Hadimin sa Malam Garba Shehu ya jajantawa ‘Yan kasuwar ‘Yankifi da ke Garin Kano game da gobarar da ci shaguna sama da 50 a karshen makon da ya wuce cikin dare ba kakautawa.

KU KARANTA: An gano 'Yan Nijar cikin sahun 'yan gudun hijiran Najeriya

Mai ba Shugaban kasar shawarar kan harkokin yada labarai ya fitar da wannan jawabi a makon nan inda yace abin bai yi wa Shugaban dadi ba. Shugaba Buhari yace wannan hadari bala’i ne musamman ta fannin tattali.

Shugaba Buhari dai ya nuna yadda gobarar ta sosa masa rai inda yace ya san irin dacin rashin da aka yi. A karshe yayi wa wanda masifar ta fada kan su addu’a da cewa Allah ya sa hakan ya zama alheri inji Hukumar NAN.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng