‘Yan Matan Sojoji sun zama kwararrun matuka jirgin saman Najeriya
- Wasu ‘Yan mata sun zama matuka jirgin saman Najeriya
- Akwai wasu maza da su ka kammala karatun tukin jirgin
- Sojojin Kasar sun yi kwas din ne a Kasar Afrika- ta- Kudu
An kafa tarihi a kwanan nan inda wasu ‘Yan Mata su ka zama Sojojin saman Najeriya. ‘Yan Matan sun zama Sojojin saman Najeriyar ne bayan da aka yi masu wani horo na musamman a kasar waje.
Sojojin dai su ne OS Ijelu da GC Nwaogwgwu da wasu mazan Sojoji har 9. Wadannan Sojoji sun samu shiga matsayin Flying Officers. A wajen taron tsohon Shugaban Hafsun Sojin kasar yana cikin masu halarta.
KU KARANTA: An karrama Shugaban Hafsun Sojin kasan Najeriya
A makon nan wasu Sojojin saman Najeriya su ka kammala wani kwas da su kayi na shekara guda cur a kasar Afrika ta kudu. Jami’an Sojojin sun yi karatu ne a Makarantar koyon tukin jirgi na Westline Aviation.
Air Chief Marshal Paul Dike ya halarci taron yaya Sojojin da aka yi a ofsihin Sojojin saman Kasar. Yanzu haka za su zama matuka jiragen saman Najeriya a gidan Soji.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng