Shan maganin bature daga masu yawo dashi a hannu, illolin hakan

Shan maganin bature daga masu yawo dashi a hannu, illolin hakan

Shin ta yaya wanda bai je makaranta ba zai sayar maka da maganin bature, ya zama likita, ya zama famasist, ya zama Nas, duk da jarin 5000? Karatun shekaru 17 duk a waje guda?

Shan maganin bature daga masu yawo dashi a hannu, illolin hakan
Shan maganin bature daga masu yawo dashi a hannu, illolin hakan

A yankin Arewa ne zaka ga masu yawo da magunguna a faranti, ko a hannu, suna yawo da shi, da sunan talla, a rana, suna sayar wa mutane, na kowacce irin cuta kuwa, suna da maganinsa.

Sun hada karatun likita, shekaru 6, da na Farmacy shekaru 6, da na Nas, shekaru 5, duk sun iya a makonni kalilan, sun san cutarka, sun san magani, sun san sau nawa zaka sha kaji sauki.

DUBA WANNAN: Wahalhalu da bautarwa a kasar Libya

Abin dariyar ma shine, har da 'yan boko a masu tare su su sayi magani, ko nasu, ko na iyalinsu. Su kuwa kamar gyada sai su zaqulo, su gaya maka yadda zaka sha, ko sau naawa, kuma kowacce irin cuta, ga dukkan alamu, su santa.

Babu kuma wata hukuma da ta damu ta hana hakan, ta basu sana'a da zasu yi, sai dai kawai su yi ta yawo da maganin a rana, duk da maganin bature bai son rana. Amma ai su ko karatun 'keep out of sunlight' basu iya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: