Jiga jigan malaman addinin Musulunci sun halarci jana’izar Sheikh Abbas Lauya
- Sheikh Abbas Isah Lauya ya rasu a garin Zaria
- Manyan Malaman jihar Kaduna sun halarci jana'izar Malamin
Wani babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Abbas Isah Lauya ya rasu a garin Zaria a ranar Juma’a 29 ga watan Satumba, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Sheikh Abbas kafin rasuwansa shine mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar jama’atil Izalatin Bidi’a wa Iqamatissunah, a lokacin da suka dunkule.
KU KARANTA: Jakadan kasar Amurka ya bayyana yawan dalibai yan Najeriya dake karatu a kasar Amurka
An yi ma marigayin jana’iza a masallacin marigayi Haruna Danja dake unguwar Tudun Wada a garin Zaria, jihar Kaduna, inda babban limamin ABU Congo Sheikh Sani Gumi ya jagoranci Sallan.
Manyan Malamai da dama sun samu halartar jana’izar, cikinsu akwai Sheikh Ahmad Gumi, Sheikh Kabiru Gombe, Sheikh Sani Yahaya Jingir da sauran manyan Malamai daga ciki da wajen Zaria.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng