Labari da dumi-dumi: ASUU ta koma aiki a Najeriya
- Kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da ta yake jiya
- A yau za a bude Jami’o’in da aka rufe tun kwanaki
- Kungiyar tace ta ba Gwamnati damar cika alkawari
Mun samu labari da dumi-dumi cewa Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a ta janye yajin aikin da ta ke yi a Najeriya a daren jiya.
Shugabannin ASUU sun dauki wannan mataki ne bayan dogon lokaci ana zantawa kamar yadda manema labarai su ka bayyana. Shugaban Kungiyar Farfesa Biodun Ogunyemi ya fadi wannan jiya a ofishin Kungiyar kwadago na NLC.
KU KARANTA: Sojojin Biyafara sun ce sun shiryawa Najeriya
Malaman Makarantar dai sun yi kwana 36 su na yaji wanda a yanzu sun yadda su koma Makarantar amma da sharadin ganin Gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka zuwa karshen watan gobe idan ba haka ba kuma a koma gidan jiya.
A yau Talata dai ASUU za tayi zama a kowane bangare inda bayan nan za a shiga bakin aiki. Tun kwanaki Ministan Ilmi Adamu Adamu ya bayyana yadda abubuwan ke tafiya ya kuma yi alkawarin kawo karshen matsalar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi wani bidiyo inda n Dalibai ke magana game da yajin aikin ASUU
Asali: Legit.ng