Kisan kare-dangi aka yi wa ‘Yan Fulani a Mambilla Inji Sojin Najeriya
– Shugaban Gundumar Soji yace kusan da gan-gan aka kashe Fulani a Mambilla
– Janar din yace da wuya ace babu hannun Hukuma da Jami’ai a barnar
– Sojan yace wadanda su ka yi wannan aiki sun fi Boko Haram barna
Shugaban Soji na Yankin Jos yace kisan kare dangi aka yi wa Fulani. Har mata masu ciki da kananan yara da shanu ba a bari ba. Bincike dai ya nuna cewa ba mamaki Hukuma na da laifi a ta’asar.
Bincike kamar yadda Shugaban Gundumar Sojin Najeriya na Runduna ta uku Birgediya Benjamin Ahanotu ya nuna kusan kisan kare dangi aka yi wa Fulani a Garin Mambilla. Abin dai har mata masu ciki da kananan yara masu shekaru 2 da shanu ba a kyale ba.
KU KARANTA: 'Yan Akwa Ibom sun ce ba ruwan su da Biyafara
Janar din yake cewa da wuya a yarda babu hannu ko sakacin Hukumar Jihar tun daga mataki na sama har kasa don ba ayi komai ba lokacin da barnar ta barke. Asali ma dai har lokacin da Soji su ka zo ana kona kauyukan Fulani. Sojan yayi tir da wannan yace har gara Boko Haram.
Kun ji cewa an kona gidaje da dama na Fulani a Mambila da ke Garin Sardauna. Mutane da yawa su ka rasa ran su inda wasu su ka samu rauni na inna-naha bayan sun tsere har ta kai wasu sun bar kasar zuwa Kamaru.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko 'Yan Najeriya za su ceci Shugaba Buhari don ya rayu
Asali: Legit.ng