Hajiya Aisha Buhari tana wakiltan Najeriya a kasar Itopiya (Hotuna)
Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta tafi kasar Itopiya domin wakiltan Najeriya a taron OAFLA da ke gudana yanzu a Addis Ababa, babban birnin kasar Itopiya.
Aisha Buhari na halartan taron tare da dukkan sauran matan shugabannin kasashen Afrika da kewaye.
Hajiya Aisha ta tafi kasar Landan kwanakin baya domin ganawa da maigidanta wanda ke jinya a Landan, amma wasu rahtotanni sun bayyana daga baya cewa bata samu daman ganawa da shi.
Kana kwamred Shehu Sani yayi kira ga sanatocin da ke kokarin tilasta shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, nada kwamitin binciken cikin al’amarin rashin lafiya Buhari.
KU KARANTA: Yakubu Gowon ya bayyana mafita a Najeriya
Yace a maimakon haka kawai su hada karfi da karfe wajen taimaka masa da addu’a.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng