Nafisa Abdullahi ta sha da ƙyar a hannun masoyanta a Katsina (Bidiyo)

Nafisa Abdullahi ta sha da ƙyar a hannun masoyanta a Katsina (Bidiyo)

- Fitacciyar yar Fim din Hausa Nafisa Abdullahi ta sha da kyar a hannun masoyanta a Katsina

- Nafisa Abdullahi ta je garin Katsina ne don yin wasan kwaikwayo yayin da lamarin ya faru

A jiya ne masoya shahararriyar yar Fim din wasan kwaikwayo na Hausa da aka fi sani da suna Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi karo da dimbin masoyanta a jihar Katsina a wani ziyarar aiki data kai a yan kwanakin nan.

Bayan sun gama wasa ne, sai masoyan nata suka dinga yin kokarin kusantar ta don daukan hoto da ita da kuma ganawa da tauraruwar ta Kannywood, amma hakan sai ya nemi ya zama matsala, inda sai da yansandan suka shiga tsakani aka samu saukin lamarin.

KU KARANTA: Dalilin da yasa shinkafar kasar waje tafi arha akan shinkafar Najeriya – Minista noma

A haka dai, da kyar aka fitar da Nafisa daga cikin taron daruruwan jama’an da suka biyo ta suka zo kallo, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Nafisa Abdullahi ta sha da ƙyar a hannun masoyanta a Katsina (Bidiyo)
Nafisa Abdullahi

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito shafinta na Instagram, Nafisa ta bayyana haka a matsayin tsananin soyayya da Katsinawa suka nuna mata, da tace yayi kama da ‘Haukan so’.

Daga karshe ta gode ma Katsinawa da karar da suka nuna mata.

Ga bidiyon nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kamata miji ya dinga bincike a wayar matarsa?

Asali: Legit.ng

Online view pixel