Nafisat Abdullahi tayi kwalkwali

Nafisat Abdullahi tayi kwalkwali

Bayan wani dan takaitaccen hutu daga masana’antan shirya fina-finai, jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta dawo da ‘kwalkwali’ a cikin wani saban shirin fim mai suna ‘Sultana’.

Nafisat Abdullahi tayi kwalkwali
Nafisat Abdullahi tayi kwalkwali a cikin fim din Sultana

Kwalin tallan shirin wasan ya nuna jarumar cikin askin kwalkwali ba tare da gashi ba a kanta.

KU KARANTA KUMA: Labari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo

Sharhi ya cika yanar gizo kan tantamar ko da gaske ne ta aske gashin nata ko kuma dai kwaliyya ne.

Wani magoyin bayan ta, Wally_Queenie, da yake sharhi a kan daya daga cikin kwalin tallar wasan da jarumar ta buga yace “shin wannan da gaske ne! ko dai aikin zane ne?

Sultana ya kasance shirin wasan Nura M. Inuwa wanda Adam A. Zango ya bada umurni.

Legit.ng ta samu labarin cewa kwanan nan jarumar ta kafa wata gidauniya na so da dariya wato (Love and Laugh foundation).

Jarumar mai shekaru 26 ta buga “Na kammala hutu, na dawo”.

KU KARANTA KUMA: EFCC: Shugaban kasa ba zai sauke Ibrahim Magu ba

Nafisa ta fara harkar shirya fina-finai a farkon 2009, sannan ta zamo mutun mai jama’a da ake ambata a Arewacin Najeriya, wasu daga cikin wasannin da ta fito a ciki sun hada da, Ummi, Ya daga Allah, Yar Agadez, Addini ko Al’Ada, Jari Hujja, Laifin Dadi, Lamiraj, Madubin Dubawa da sauran su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon wasu mata dake sana'ar gyaran motoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel